40
1 Ubangiji ya ce wa Ayuba,
2 “Mai neman sa wa wani laifi zai iya ja da Maɗaukaki?
Bari mai tuhumar Allah yă amsa masa.”
3 Sai Ayuba ya amsa wa Ubangiji,
4 “Ai, ni ba a bakin kome nake ba ne, ta yaya zan iya amsa maka?
Na rufe bakina da hannuna.
5 Na yi magana sau ɗaya amma ba ni da amsa,
sau biyu, amma ba zan ƙara cewa kome ba.”
6 Sa’an nan Ubangiji ya yi wa Ayuba magana ta cikin guguwa,
7 “Ka tashi tsaye ka tsaya da ƙarfi kamar namiji;
zan yi maka tambaya
kuma za ka amsa mini.
8 “Ko za ka ƙi yarda da shari’ata?
Za ka ba ni laifi don ka nuna kai marar laifi ne?
9 Ko hannunka irin na Allah ne,
kuma ko muryarka za tă iya tsawa kamar ta Allah?
10 Sai ka yi wa kanka ado da ɗaukaka da girma,
ka yafa daraja da muƙami.
11 Ka saki fushinka,
ka dubi dukan wani mai girman kai ka wulaƙanta shi.
12 Ka dubi duk wani mai girman kai ka ƙasƙantar da shi,
ka tattake mugaye a inda ka tsaya.
13 Ka bizne su duka tare
ka rufe fuskokinsu a cikin kabari.
14 Sa’an nan ni kaina zan shaida maka cewa
hannun damanka zai iya cetonka.
15 “Dubi dorina,
wadda na halicce ku tare
kuma ciyawa take ci kamar sa.
16 Ga shi ƙarfinta yana a ƙugunta
ikonta yana cikin tsokar cikinta.
17 Wutsiyarta tana da ƙarfi kamar itacen al’ul;
jijiyoyin cinyoyinta suna haɗe a wuri ɗaya.
18 Ƙasusuwanta bututun tagulla ne,
haƙarƙarinta kamar sandunan ƙarfe.
19 Tana ta farko cikin ayyukan Allah,
Mahaliccinta kaɗai yake iya tunkarar ta da takobi.
20 Tuddai su suke tanada mata abinci
a inda duk namun jeji suke wasa.
21 Tana kwanciya a ƙarƙashin inuwar itacen lotus
ta ɓuya cikin kyauro da fadama.
22 Inuwa ta rufe ta da ƙaddaji,
itatuwan wardi na rafi, sun kewaye ta.
23 Sa’ad da kogi ya cika yana hauka, ba tă damu ba;
ba abin da zai same ta ko da a gaban bakinta Urdun yake wucewa.
24 Ko akwai wanda zai iya kama ta ba ta kallo,
ko kuma a kama ta da tarko a huda hancinta?