39
1 “Ka san lokacin da awakin kan dutse suke haihuwa?
Ko ka taɓa lura da yadda batsiya take haihuwa?
2 Kana ƙirga watanni nawa suke yi kafin su haihu?
Ka san lokacin da suke haihuwa?
3 Suna kwanciya su haifi ’ya’yansu;
naƙudarsu ta ƙare bayan sun haihu.
4 ’Ya’yansu suna girma kuma suna girma cikin ƙarfi a jeji;
sukan tafi ba su dawowa.
5 “Wane ne yake sakin jakin dawa yă bar shi?
Wane ne yake kunce igiyoyinsu?
6 Na sa jeji yă zama gidansa
ƙasar gishiri kuma ta zama wurin zamansa.
7 Yana dariyar hargitsin da yake faruwa a cikin gari;
ba ya jin tsawar mai tuƙa shi.
8 Yana kiwo a kan tuddai don abincinsa
yana neman kowane ɗanyen abu mai ruwan ciyawa.
9 “Ko ɓauna zai yarda yă zauna a wurin sa wa dabbobi abinci?
Zai tsaya a ɗakin dabbobinka da dare?
10 Ko za ka iya daure shi da igiya a kwarin kunya?
Zai yi maka buɗar gonarka?
11 Ko za ka dogara da shi don yawan ƙarfinsa?
Za ka bar masa nauyin aikinka?
12 Ko za ka amince da shi yă kawo maka hatsinka gida
yă tattara shi a masussuka?
13 “Fikafikan jimina suna bugawa cike da farin ciki
amma ba za su gwada kansu da fikafikan da na shamuwa ba.
14 Tana sa ƙwai nata a ƙasa
kuma ta bar su su yi ɗumi a cikin ƙasa,
15 ba tă damu ko za a taka su a fasa su,
ko waɗansu manyan dabbobi za su tattake su.
16 Tana tsananta wa ’ya’yanta kamar ba nata ba
ba tă damu da wahalar da ta sha ba.
17 Gama Allah bai ba ta hikima ba
ko kuma iya fahimta.
18 Duk da haka sa’ad da ta buɗe fikafikanta ta shara da gudu
tana yi wa doki da mai hawansa dariya.
19 “Ko kai ne kake ba doki ƙarfinsa
kai kake rufe wuyansa da geza mai yawa?
20 Ko kai kake sa shi yă yi tsalle kamar fāra,
ba ya jin tsoro sai dai a ji tsoronsa.
21 Yana takawa da ƙarfi
yana jin daɗin ƙarfinsa yana shiga filin yaƙi gabagadi.
22 Yana yi wa tsoro dariya
ba ya jin tsoron kome; ba ya guje wa takobi.
23 Kwari a baka yana lilo a gabansa
kibiya da māshi suna wuce kansa.
24 Yana kartar ƙasa da ƙarfi;
ba ya iya tsayawa tsab sa’ad da ya ji busar ƙaho.
25 Da jin ƙarar ƙaho sai ya ce, ‘Yauwa!’
Ya ji ƙanshin yaƙi daga nesa,
da ihun shugabannin yaƙi.
26 “Ko ta wurin hikimarka ce shirwa take firiya
take kuma baza fikafikanta zuwa kudu?
27 Ko da umarninka ne shaho yake firiya
ya kuma yi sheƙarsa a can sama?
28 Yana zama a kan dutse yă zauna a wurin da dare;
cikin duwatsu ne wurin zamansa.
29 Daga can yake neman abincinsa;
idanunsa suna gani daga nesa.
30 ’Ya’yansa suna shan jini,
inda akwai waɗanda aka kashe nan za a same shi.”