21
Sabuwar sama da sabuwar duniya
1 Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. 2 Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. 3 Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, “Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. 4 Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe.”
5 Wannan da yake zaune a kursiyin ya ce. “Ina yin kome sabo!” Sai ya ce, “Rubuta wannan, domin waɗannan kalmomi amintattu ne gaskiya ne kuma.”
6 Ya ce mini, “An gama. Ni ne Alfa da kuma Omega, na Farko da kuma na Ƙarshe. Duk mai jin ƙishirwa zan ba shi abin sha kyauta daga maɓulɓular ruwan rai. 7 Duk wanda ya ci nasara zai gāji dukan wannan, zan kuma zama Allahnsa, shi kuma zai zama ɗana. 8 Amma matsorata, da marasa bangaskiya, masu ƙazanta, masu kisankai, masu fasikanci, masu sihiri, masu bautar gumaka da dukan maƙaryata, wurinsu zai kasance a cikin tafkin wutar da yake farar wuta mai ci. Wannan fa ita ce mutuwa ta biyu.”
9 Ɗaya daga cikin mala’ikun nan bakwai masu kwanonin nan bakwai cike da annoban nan bakwai na ƙarshe, ya zo ya ce mini “Zo, zan nuna maka amaryar, matar Ɗan Ragon.” 10 Ya kuwa ɗauke ni cikin Ruhu zuwa wani babban dutse mai tsayi, ya kuma nuna mini Birni Mai Tsarki, Urushalima, tana saukowa daga sama, daga Allah. 11 Ya haskaka da ɗaukakar Allah, haskensa kuwa ya yi kamar lu’ulu’u mai daraja sosai, kamar yasfa, yana ƙyalƙyali kamar madubi. 12 Yana da babbar katanga mai tsayi, mai ƙofofi goma sha biyu, da kuma mala’iku goma sha biyu a ƙofofin. A bisa ƙofofin an rubuta sunayen kabilu goma sha biyu na Isra’ila. 13 Akwai ƙofofi uku a gabas, uku a arewa, uku a kudu, uku kuma a yamma. 14 An gina katangar birnin a kan tushen gini goma sha biyu, a kansu kuwa akwai sunayen manzannin sha biyu na Ɗan Ragon.
15 Mala’ikan da ya yi magana da ni yana da sandan awo na zinariya don awon birnin, ƙofofinsa, da kuma katangarsa. 16 Birnin murabba’i ne, tsayinsa daidai ne da fāɗinsa. Ya auna birnin da sandarsa ya kuwa sami mil 1,400 (wajen kilomita 2,200) tsawonsa, fāɗinsa da kuma tsayinsa daidai suke. 17 Ya auna katangarsa ya kuma sami ƙaurinta kamun 144, bisa ga ma’aunin mutum, wanda mala’ikan ya yi amfani da shi. 18 An yi katangar da yasfa, birnin kuma da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi. 19 Tushen ginin katangar birnin kuwa an yi masa adon da kowane irin dutse mai daraja. Tushe na farko an yi shi yasfa, na biyu saffaya, na uku agat, na huɗu zumurrudu, 20 na biyar onis, na shida yakutu, na bakwai kirisolit, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofuras, na goma sha ɗaya yasin, na goma sha biyu kuma ametis. 21 Ƙofofi goma sha biyun nan lu’ulu’ai goma sha biyu ne, kowace ƙofa an yi ta da lu’ulu’u guda. Babban titin birnin kuwa an yi shi da zinariya zalla, yana kuma ƙyalli kamar madubi.
22 Ban ga haikali a cikin birnin ba, domin Ubangiji Allah Maɗaukaki da kuma Ɗan Ragon ne haikalin birnin. 23 Birnin ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, gama ɗaukakar Allah tana ba shi haske, Ɗan Ragon kuwa shi ne fitilar birnin. 24 Al’ummai za su yi tafiya cikin hasken birnin, sarakunan duniya kuma za su kawo darajarsu cikin birnin. 25 Ba za a taɓa rufe ƙofofin birnin da rana ba, gama ba za a yi dare a can ba. 26 Za a kawo ɗaukaka da girmar al’ummai a cikin birnin. 27 Babu wani abu marar tsarkin da zai taɓa shiga cikin birnin, babu kuma wani mai aikata abin kunya ko ruɗi da zai shiga, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a cikin littafin rai na Ɗan Ragon.