Zabura 148
Yabi Ubangiji daga sammai,
yabe shi a bisa sammai.
2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa,
yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.
3 Yabe shi, rana da wata,
yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.
4 Yabe shi, ku bisa sammai
da kuma ku ruwan bisa sarari.
5 Bari su yabi sunan Ubangiji,
gama ya umarta aka kuwa halicce su.
6 Ya sa su a wurarensu har abada abadin;
ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.
7 Yabi Ubangiji daga duniya,
ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,
8 walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai,
hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,
9 ku duwatsu da dukan tuddai,
itatuwa masu ’ya’ya da dukan al’ul,
10 namun jeji da dukan dabbobin gida,
ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,
11 sarakunan duniya da dukan al’ummai,
ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,
12 samari da ’yan mata,
tsofaffi da yara.
13 Bari su yabi sunan Ubangiji,
gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka;
darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.
14 Ya tayar wa mutanensa ƙaho,† Ƙaho a nan na nuna wani mai ƙarfi, wato, sarki.
yabon dukan tsarkakansa,
na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa.
Yabi Ubangiji.
*Zabura 148:1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya; haka ma a aya 14.
†Zabura 148:14 Ƙaho a nan na nuna wani mai ƙarfi, wato, sarki.