Zabura 144
Ta Dawuda.
1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena,
wanda ya horar da hannuwana don yaƙi,
yatsotsina don faɗa.
2 Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata,
katangata da mai cetona,
garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi,
wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.
3 Ya Ubangiji, wane ne mutum da ka kula da shi,
ɗan mutum da har za ka yi tunaninsa?
4 Mutum yana kama da numfashi;
kwanakinsa suna wucewa kamar inuwa.
5 Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko;
ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi.
6 Ka aiko da walƙiya ka watsar da abokan gāba;
ka karɓa kibiyoyinka ka sa su gudu.
7 Ka miƙa hannunka daga bisa;
ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni
daga manyan ruwaye,
daga hannuwan baƙi
8 waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya,
waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.
9 Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah;
a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi,
10 ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara,
wanda ya cece bawansa Dawuda.
Daga takobin kisa. 11 Ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni
daga hannuwan baƙi
waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya,
waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.
12 Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu
za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su,
’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai
da sassaƙa don adon fada.
13 Rumbunanmu za su cika
da kowane irin tanadi.
Tumakinmu za su ƙaru ninki dubu,
ninki dubu goma-goma a filayenmu;
14 shanunmu za su ja kaya masu nauyi.* Ko kuwa manyanmu za su kahu daram
Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba,
ba zuwan zaman bauta,
ba jin kukan damuwa a titunanmu.
15 Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka;
masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji.