Zabura 71
1 A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka;
kada ka taɓa sa in sha kunya.
2 Ka kuɓutar da ni ka cece ni cikin adalcinka;
ka juya kunnenka gare ni ka kuma cece ni.
3 Ka zama dutsena da kagarata,
inda kullum zan je.
Ka ba da umarni a cece ni,
gama kai ne dutsen ɓuyana da katangata.
4 Ka cece ni, ya Allahna, daga hannun mugaye,
da kuma daga ikon mugaye da masu mugunta.
5 Gama kai ne abin sa zuciyata, ya Ubangiji Mai Iko Duka,
ƙarfin zuciyata tun ina yaro.
6 Daga haihuwa na dogara gare ka;
kai ka kawo ni daga cikin mahaifiyata.
Kullayaumi zan yabe ka.
7 Na zama kamar abin sa zuciya ga yawanci,
amma kai ne katangata mai ƙarfi.
8 Bakina ya cika da yabonka,
ina furta darajarka dukan yini.
9 Kada ka yar da ni sa’ad da na tsufa;
kada ka yashe ni sa’ad da ƙarfina ya ƙare.
10 Gama abokan gābana suna magana a kaina;
waɗanda suke jira su kashe ni suna haɗa baki tare.
11 Suna cewa, “Allah ya yashe shi;
mu fafare shi mu kama shi,
gama ba wanda zai kuɓutar da shi.”
12 Kada ka yi nisa da ni, ya Allah;
zo da sauri, ya Allahna, ka taimake ni.
13 Bari masu zagina su hallaka da kunya;
bari waɗanda suke so su cutar da ni
su sha ba’a da kuma kunya.
14 Amma game da ni, kullayaumi zan kasance da sa zuciya;
zan yabe ka sau da sau.
15 Bakina zai ba da labarin adalcinka,
zai yi maganar cetonka dukan yini,
ko da yake ban san yawansa ba.
16 Zan zo in furta in kuma yi shelar ayyukanka masu girma, ya Ubangiji Mai Iko Duka;
zan yi shelar adalcinka, naka kaɗai.
17 Tun ina yaro, ya Allah, ka koya mini
har wa yau ina furta ayyukanka masu banmamaki.
18 Ko sa’ad da na tsufa da furfura,
kada ka yashe ni, ya Allah,
sai na furta ikonka ga tsara mai zuwa,
ƙarfinka ga dukan waɗanda suke zuwa.
19 Adalcinka ya kai sararin sama, ya Allah,
kai da ka yi manyan abubuwa.
Wane ne kamar ka, ya Allah?
20 Ko da yake ka sa na ga wahaloli,
masu yawa da kuma masu ɗaci,
za ka sāke mayar mini da rai;
daga zurfafan duniya
za ka sāke tā da ni.
21 Za ka ƙara girmana
ka sāke ta’azantar da ni.
22 Zan yabe ka da garaya
saboda amincinka, ya Allah;
zan rera yabo gare ka da molo,
Ya Mai Tsarki na Isra’ila.
23 Leɓunana za su yi sowa don farin ciki
sa’ad da na rera yabo gare ka,
ni, wanda ka fansa.
24 Harshena zai ba da labarin ayyukanka masu adalci
dukan yini,
gama waɗanda suka so su cutar da ni
sun sha kunya suka kuma rikice.