Zabura 12
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit.* Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar kiɗi ce. Zabura ta Dawuda.
1 Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma;
masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.
2 Kowa yana yi wa maƙwabcinsa ƙarya;
zaƙin bakinsu maganar ƙarya ce
suna cike da ruɗu a zukatansu.
3 Bari Ubangiji yă yanke dukan zaƙin bakinsu
da kuma kowane harshe mai fariya,
4 masu cewa,
“Da harsunanmu za mu yi nasara;
leɓunanmu za su kāre mu, wane ne maigidanmu?”
5 “Saboda danniyar marasa ƙarfi da kuma nishin masu bukata,
zan tashi yanzu,” in ji Ubangiji.
“Zan kāre su daga masu yin musu sharri.”
6 Kalmomin Ubangiji kuwa ba su da kuskure,
kamar azurfan da aka tace cikin matoyan yumɓu,
aka tsabtacce sau bakwai.
7 Ya Ubangiji, za ka kiyaye mu lafiya
ka tsare mu daga irin mutanen nan har abada.
8 Mugaye suna yawo a sake
sa’ad da ake girmama abin da ba shi da kyau a cikin mutane.