20
Misalin ma’aikata a gonar inabi
1 “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa. 2 Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.
3 “Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome. 4 Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’ 5 Saboda haka suka tafi.
“Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka. 6 Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’
7 “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’
“Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’
8 “Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’
9 “Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda. 10 Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda. 11 Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar. 12 Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’
13 “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba? 14 Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka. 15 Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’
16 “Saboda haka fa, na ƙarshe za su zama na farko, na farko kuma su zama na ƙarshe.”
Yesu ya sāke yin zancen mutuwarsa
(Markus 10.32-34; Luka 18.31-34)
17 To, da Yesu yana haurawa zuwa Urushalima, sai ya ja almajiran nan goma sha biyu gefe, ya ce musu, 18 “Za mu haura zuwa Urushalima, za a kuma bashe Ɗan Mutum ga manyan firistoci da malaman dokoki. Za su yi masa hukuncin kisa 19 za su kuma bashe shi ga Al’ummai su yi masa ba’a, su yi masa bulala, su kuma gicciye shi. A rana ta uku kuma a tashe shi!”
Roƙon mahaifiya
(Markus 10.35-45)
20 Sai mahaifiyar ’ya’yan Zebedin nan ta zo wurin Yesu tare da ’ya’yanta, da ta durƙusa a ƙasa, sai ta roƙe shi yă yi mata wani abu.
21 Ya yi tambaya ya ce, “Mene ne kike so?”
Ta ce, “Ka sa daga cikin ’ya’yan nan nawa biyu, ɗaya yă zauna a damarka, ɗaya kuma a hagunka, a mulkinka.”
22 Yesu ya ce musu, “Ba ku san abin da kuke roƙo ba. Za ku iya sha daga kwaf da zan sha?”
Suka amsa, “Za mu iya.”
23 Yesu ya ce musu, “Tabbatacce za ku sha daga kwaf na, sai dai zama a damana, ko haguna, ba ni nake da izinin bayarwa ba. Waɗannan wurare na waɗanda Ubana ya shirya wa ne.”
24 Da goman suka ji haka, sai suka yi fushi da ’yan’uwan nan biyu. 25 Yesu ya kira su wuri ɗaya ya ce, “Kun san cewa masu mulkin Al’ummai sukan nuna musu iko, hakimansu kuma sukan gasa musu iko. 26 Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole yă zama bawanku, 27 kuma duk mai son zama shugaba, dole yă zama bawanku, 28 kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yă yi bauta, yă kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa.”
Makafi biyu sun sami ganin gari
(Markus 10.46-52; Luka 18.35-43)
29 Sa’ad da Yesu da almajiransa suke barin Yeriko, sai wani babban taro ya bi shi. 30 Makafi biyu kuwa suna zaune a bakin hanya, da suka ji cewa Yesu yana wucewa, sai suka ɗaga murya suka ce, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”
31 Mutane suka tsawata musu, suka ce musu su yi shiru. Sai suka ƙara ɗaga murya suna cewa, “Ubangiji, Ɗan Dawuda, ka ji tausayinmu!”
32 Yesu ya tsaya ya kira su. Ya tambaye su, “Me kuke so in yi muku?”
33 Suka amsa suka ce, “Ubangiji, muna so mu sami ganin gari.”
34 Sai Yesu ya ji tausayinsu, ya taɓa idanunsu. Nan da nan kuwa suka sami ganin gari, suka kuma bi shi.