18
Bildad
1 Sai Bildad mutumin Shuwa ya amsa,
2 “Yaushe za ka gama maganganun nan?
Ka dawo da hankalinka sa’an nan za mu iya yin magana.
3 Don me muke kamar shanu a wurinka,
ka ɗauke mu mutanen wofi?
4 Kai da ka yayyage kanka don haushi,
za a yashe duniya saboda kai ne?
Ko kuma duwatsu za su matsa daga wurinsu?
5 “An kashe fitilar mugu;
harshen wutarsa ya daina ci.
6 Wutar cikin tentinsa ta zama duhu;
fitilar da take kusa da shi ta mutu.
7 Ƙarfin takawarsa ya ragu;
dabararsa ta ja fāɗuwarsa.
8 Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga,
yana ta yawo a cikin ragar.
9 Tarko ya kama ɗiɗɗigensa;
tarko ya riƙe shi kam.
10 An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa;
an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.
11 Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe
yana bin shi duk inda ya je.
12 Masifa tana jiransa;
bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.
13 Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa;
ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.
14 An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa
aka sa shi tsoro sosai.
15 Wuta ta cinye tentinsa;
farar wuta ta rufe wurin da yake zama.
16 Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa
rassansa sun mutu a sama.
17 An manta da shi a duniya;
ba wanda yake ƙara tunawa da shi.
18 An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu,
an kore shi daga duniya.
19 Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa,
ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.
20 Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi;
tsoro ya kama mutanen gabas.
21 Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake,
haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”