20
Irmiya da Fashhur
1 Da firist nan Fashhur ɗan Immer, babban ma’aikaci a cikin haikalin Ubangiji, ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan abubuwa, 2 sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji. 3 Kashegari, sa’ad da Fashhur ya fitar da shi daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashhur ba, amma ya ba ka suna Magor-Missabib.* Magor-Missabib yana nufin razana ta kowace fuska. 4 Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi. 5 Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon. 6 Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”
Damuwar Irmiya
ka fi ni ƙarfi, ka kuwa yi nasara.
Na zama abin dariya dukan yini;
kowa yana yi mini ba’a.
8 Duk sa’ad da na yi magana, nakan tā da murya
ina furta hargitsi da hallaka.
Haka maganar Ubangiji ta kawo mini
zagi da reni dukan yini.
9 Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba
ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,”
sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta,
wutar da aka kulle a ƙasusuwana.
Na gaji da danne ta a cikina;
tabbatacce ba zan iya ba.
10 Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa,
“Razana ta kowace fuska!
Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!”
Dukan abokaina
suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa,
“Mai yiwuwa a ruɗe shi;
sai mu yi nasara a kansa
mu ɗau fansa a kansa.”
11 Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi;
saboda haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe ba kuwa za su yi nasara ba.
Za su fāɗi su kuma sha mummunar kunya;
ba za a taɓa manta da rashin bangirmansu ba.
12 Ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake gwada adali
kana bincika zuciya duk da tunani,
bari in ga sakayyarka a kansu,
gama a gare ka na miƙa damuwata.
13 Ku rera ga Ubangiji!
Ku yabi Ubangiji!
Ya kuɓutar da ran mabukaci
daga hannuwan mugaye.
14 La’ananniya ce ranar da aka haife ni!
Kada ranar da mahaifiyata ta haife ni ta zama mai albarka!
15 La’ananne ne mutumin da ya kawo wa mahaifina labari,
wanda ya sa shi ya yi murna cewa, “An haifa maka yaro, ɗa namiji!”
16 Bari mutumin ya zama kamar garuruwan
da Ubangiji ya tumɓuke ba tausayi.
Bari yă ji kuka da safe
kururuwan yaƙi kuma da tsakar rana.
17 Gama bai kashe ni a cikin ciki ba,
da ma ya sa cikin mahaifiyata ya zama kabarina,
cikinta ya fadada har abada.
18 Me ya sa na ma fito daga cikin ciki
in ga wahala da baƙin ciki
in kuma ƙare kwanakina da kunya?