10
Allah da kuma gumaka
1 Ku ji abin da Ubangiji yana ce muku, ya gidan Isra’ila. 2 Ga abin da Ubangiji yana cewa,
“Kada ku koyi hanyoyin al’ummai
ko ku razana game da alamun sararin sama,
ko da yake al’ummai sun razana saboda su.
3 Gama al’adun mutane banza ne;
sukan yanke itace daga kurmi,
sai mai sassaƙa yă sassaƙa shi da gizago.
4 Sukan yi masa ado da azurfa da kuma zinariya;
sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi,
don kada yă fāɗi.
5 Kamar dodon gona cikin gonar kabewa,
haka gumakansu ba sa iya magana;
dole a yi ta ɗaukansu
domin ba za su iya tafiya ba.
Kada ku ji tsoronsu;
ba za su iya yi wa wani lahani ba
ba sa iya yin wani abin kirki.”
6 Babu wani kamar ka, ya Ubangiji;
kai mai girma ne,
kuma sunanka yana da girma da kuma iko.
7 Wane ne ba zai girmama ka ba,
Ya Sarkin al’ummai?
Tsoronka wajibi ne.
A cikin dukan masu hikima na al’ummai
kuma cikin dukan mulkokinsu,
babu kamar ka.
8 Dukansu marasa azanci ne wawaye;
gumakan itacen banza ne suke koya musu.
9 An kawo ƙeraren azurfa daga Tarshish
zinariya kuma daga Ufaz.
Abin da gwani da maƙerin zinariya suka yi
sa’an nan aka yi masa ado da mulufi da shunayya
dukan aikin gwanaye.
10 Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya;
shi ne Allah mai rai, madawwamin sarki.
Sa’ad da ya yi fushi, ƙasa takan girgiza;
al’ummai ba sa iya jure da hasalarsa.
11 “Ka faɗa musu wannan, ‘Waɗannan alloli, waɗanda ba su yi sammai da ƙasa ba, za su hallaka daga duniya da kuma daga ƙarƙashin sammai.’ ”* Wannan sashe na wannan aya yana a harshen Arameya ne.
12 Amma Allah ya yi duniya ta wurin ikonsa;
ya kafa duniya ta wurin hikimarsa
ya shimfiɗa sammai ta wurin fahiminsa.
13 Sa’ad da ya yi tsawa, ruwaye a cikin sammai sukan yi ƙugi;
yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya.
Yakan aiki walƙiya da ruwan sama
ya fitar da iska daga gidajen ajiyarsa.
14 Kowa marar azanci ne, marar ilimi;
kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa.
Siffofinsa ƙarya ne;
ba su da numfashi a cikinsu.
15 Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne;
Sa’ad da hukuncinsu ya yi za su lalace.
16 Shi da yake Rabon Yaƙub ba kamar waɗannan yake ba,
gama shi ne Mahaliccin abubuwa duka,
har da Isra’ila, kabilar gādonsa
Ubangiji Maɗaukaki ne sunansa.
Hallaka mai zuwa
17 Ku tattara kayayyakinku don ku bar ƙasar,
ku da kuke zaune a wurin da aka kewaye da yaƙi.
18 Gama haka Ubangiji ya faɗa,
“A wannan lokaci zan jefar
da waɗanda suke zaune a ƙasar;
zan kawo damuwa a kansu
domin a kama su.”
19 Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini!
Raunina ba mai warkewa ba ne!
Duk da haka na ce wa kaina,
“Wannan ciwona ne, dole kuma in jure da shi.”
20 An lalatar da tentina;
dukan igiyoyinsa sun tsintsinke.
’Ya’yana maza sun bar ni ba sa nan;
ba wanda aka bari da zai kafa tentina
ko ya kafa mini mafaka.
21 Makiyaya marasa azanci ne
kuma ba sa neman nufin Ubangiji;
saboda haka ba sa nasara
dukan garkensu kuwa ya watse.
22 Ku saurara! Rahoto yana zuwa
babban hargitsi daga ƙasar arewa!
Zai mai da garuruwan Yahuda kufai,
mazaunin diloli.
Addu’ar Irmiya
23 Na sani, ya Ubangiji, cewa ran mutum ba nasa ba ne;
ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba.
24 Ka yi mini gyara, Ubangiji, amma fa da adalci kaɗai
ba cikin fushinka ba,
don kada ka wofinta ni.
25 Ka zuba hasalarka a kan al’umman
da ba su san ka ba,
a kan mutanen da ba sa kira bisa sunanka.
Gama sun cinye Yaƙub;
sun cinye shi gaba ɗaya
suka kuma lalace wurin zamansa.