53
1 Wa ya gaskata saƙonmu
kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?
2 Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi,
kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa.
Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu,
babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa.
3 Mutane suka rena shi suka ƙi shi,
mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala.
Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi
aka rena shi aka yi banza da shi.
4 Tabbatacce ya ɗauki cututtukanmu
ya kuma daure da baƙin cikinmu
duk da haka muka ɗauka Allah ya hukunta shi ne,
ya buge shi ya kuma sa ya sha azaba.
5 Amma aka yi masa rauni saboda laifofinmu,
aka ƙuje shi saboda kurakuranmu;
hukuncin da ya kawo mana salama ya kasance a kansa,
kuma ta wurin mikinsa ya sa muka warke.
6 Dukanmu, muna kama da tumakin da suka ɓata,
kowannenmu ya kama hanyarsa;
Ubangiji kuwa ya sa hukunci ya auko a kansa
hukuncin da ya wajaba a kanmu.
7 Aka wulaƙanta shi aka kuma yi masa azaba,
duk da haka bai buɗe bakinsa ba;
aka kai shi kamar ɗan rago zuwa wurin yanka,
kuma kamar tunkiya a gaban masu askinta tana shiru,
haka bai buɗe bakinsa ba.
8 Da wulaƙanci* Ko kuma Daga kamawa da kuma hukunci aka ɗauke shi aka tafi.
Wa kuwa zai yi maganar zuriyarsa?
Gama an kawar da shi daga ƙasar masu rai;
saboda laifin mutanena aka kashe shi.† Ko kuwa kawar. Duk da haka wane ne a zamaninsa ya kula cewa an yanke shi daga ƙasar masu rai saboda laifin mutanena, waɗanda ya kamata su sha bugun?
9 Aka yi jana’izarsa tare da mugaye,
aka binne shi tare da masu arziki,
ko da yake bai taɓa yin wani tashin hankali ba,
ko a sami ƙarya a bakinsa.
10 Duk da haka nufin Ubangiji ne a ƙuje shi yă kuma sa yă sha wahala,
kuma ko da yake Ubangiji ya sa ransa ya zama hadaya don zunubi,
zai ga zuriyarsa zai kuma kawo masa tsawon rai,
nufin Ubangiji kuma zai yi nasara a hannunsa.
11 Bayan wahalar ransa,
zai ga hasken rai, ya kuma gamsu;
ta wurin saninsa bawana mai adalci zai ’yantar da mutane masu yawa,
zai kuma ɗauki laifofinsu.
12 Saboda haka zan ba shi rabo tare da manya,
zai kuma raba ganima tare da masu ƙarfi,
domin ya ba da ransa har mutuwa,
aka kuma lissafta shi tare da masu laifofi.
Gama ya ɗauki zunubin mutane masu yawa,
ya kuma yi roƙo saboda laifofinsu.