37
An yi faɗin ceton Urushalima
(2 Sarakuna 19.1-13)
1 Sa’ad da Sarki Hezekiya ya ji haka, sai ya kyakkece rigunansa ya kuma sanya tsummoki ya tafi ya shiga haikalin Ubangiji. 2 Ya aiki Eliyakim sarkin fada, Shebna magatakarda da kuma manyan firistoci, duka sanye da tsummoki, wurin Ishaya ɗan Amoz. 3 Suka faɗa masa cewa, “Ga abin da Hezekiya ya ce wannan rana ce ta baƙin ciki da tsawatawa da shan kunya, sai ka ce sa’ad da ’ya’ya kan zo matakin haihuwa sa’an nan a rasa ƙarfin haihuwarsu. 4 Mai yiwuwa Ubangiji Allahnka zai ji maganganun sarkin yaƙin da maigidansa, sarkin Assuriya, ya aika don yă zagi Allah mai rai, ya kuma tsawata masa saboda maganganun da Ubangiji Allahnka ya ji. Saboda haka ka yi addu’a saboda raguwar da suke da rai.”
5 Sa’ad da shugabannin Sarki Hezekiya suka zo wurin Ishaya, 6 sai Ishaya ya ce musu, “Ku faɗa wa maigidanku cewa, ‘Ga abin da Ubangiji ya faɗa. Kada ka ji tsoron abin da ka ji, maganganun nan da bayin sarkin Assuriya suka yi mini saɓo. 7 Ka saurara! Zan sa ruhuna a cikinsa saboda sa’ad da ya ji wani labari, zai koma zuwa ƙasarsa, a can kuwa zan sa a kashe shi da takobi.’ ”
8 Sa’ad da sarkin yaƙin ya ji cewa sarkin Assuriya ya bar Lakish, sai ya janye ya kuma sami sarki yana yaƙi da Libna.
9 To, fa, Sennakerib ya sami labari cewa Tirhaka, mutumin Kush sarkin Masar, yana fitowa don yă yi yaƙi da shi. Sa’ad da ya ji haka, sai ya aiki jakadu zuwa wurin Hezekiya da wannan magana. 10 “Ku faɗa wa Hezekiya sarkin Yahuda cewa kada ka bar allahn da ka dogara a kai ya ruɗe ka sa’ad da ya ce, ‘Ba za a ba da Urushalima ga sarkin Assuriya ba.’ 11 Tabbatacce ka ji abin da sarakunan Assuriya suka aikata ga dukan ƙasashe, suna hallaka su tas. Kai kuwa za ka tsira ne? 12 Allolin al’umman da kakannina suka hallaka sun cece su ne, allolin Gozan, Haran, Rezef da kuma na mutanen Eden waɗanda suke zama a Tel Assar? 13 Ina sarkin Hamat yake, sarkin Arfad fa, sarkin Sefarfayim, ko na Hena ko na Iffa?”
Addu’ar Hezekiya
(2 Sarakuna 19.14-19)
14 Hezekiya ya karɓi wasiƙar daga jakadun ya karanta ta. Sa’an nan ya haura zuwa haikalin Ubangiji ya shimfiɗa ta a gaban Ubangiji. 15 Sai Hezekiya ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, 16 “Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, zaune a tsakanin kerubobi, kai kaɗai ne Allah a kan dukan masarautan duniya. 17 Ka kasa kunne, ya Ubangiji, ka kuma ji; ka buɗe idanunka, ya Ubangiji, ka kuma gani; ka saurara ga dukan maganganun da Sennakerib ya aika don yă zagi Allah mai rai.
18 “Gaskiya ce, ya Ubangiji, cewa sarakunan Assuriyawa sun mai da dukan waɗannan mutane da ƙasashensu kango. 19 Sun jefar da gumakansu cikin wuta suka kuma hallaka su, gama su ba alloli ba ne itace ne kawai da dutse, da hannuwan mutane suka sarrafa. 20 Yanzu, ya Ubangiji Allahnmu, ka cece mu daga hannunsa, saboda masarautai a duniya su san cewa kai kaɗai ne, ya Ubangiji, Allah.”
Fāɗuwar Sennakerib
(2 Sarakuna 19.20-34)
21 Sa’an nan Ishaya ɗan Amoz ya aika da saƙo wa Hezekiya cewa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, ya faɗa. Saboda ka yi addu’a gare ni game da Sennakerib sarkin Assuriya, 22 ga abin da maganar Ubangiji ya faɗa a kansa,
“Budurwa Diyar Sihiyona
ta rena tana kuma maka ba’a.
Diyar Urushalima
tana kada kai yayinda kake gudu.
23 Wane ne ka zargi ka kuma yi wa saɓo?
A kan wa ka tā da muryarka
ka kuma daga idanu cikin fariya?
A kan Mai Tsarkin nan na Isra’ila!
24 Ta wurin jakadunka
ka jibge zage-zage a kan Ubangiji.
Ka kuma ce,
‘Da kekunan yaƙina masu yawa
na hau ƙwanƙolin duwatsu,
ƙwanƙolin mafi tsayi na Lebanon.
Na sassare al’ul mafi tsayi
fir mafi kyau.
Na kai can wuri mafi nisa na kurminsa.
25 Na haƙa rijiyoyi a baƙuwar ƙasa
na kuma sha ruwa a can.
Da tafin ƙafafuna
na busar da dukan rafuffukan Masar.’
26 “Ba ka ji ba cewa
tun dā can na shirya ya zama haka?
A kwanakin dā na kafa shi;
yanzu na sa ya faru,
cewa ka mai da birane masu mafaka
zuwa tsibin ɓuraguzai.
27 Mutanensu, suka rasa ƙarfi,
sun firgita suka kuma sha kunya.
Suka zama kamar tsire-tsire a gona,
kamar tsire-tsiren ta suka tohu,
kamar ciyawar da ya tsiro a kan rufi,
wadda zafi ya yi wa ƙuna kafin tă yi girma.
28 “Amma na san inda kake zama
da sa’ad da kakan fita ka kuma koma
da yadda ka harzuƙa gāba da ni.
29 Saboda ka harzuƙa gāba da ni
kuma saboda girmankanka ya kai kunnuwana,
zan sa ƙugiya a hancinka
linzamina a bakinka,
zan kuma sa ka koma
ta hanyar da ka zo.
30 “Wannan zai zama alama gare ka, ya Hezekiya,
“Wannan shekara za ka ci abin da ya yi girma da kansa,
shekara ta biyu kuma abin da ya tsiro daga wancan.
Amma a shekara ta uku za ka yi shuki ka kuma girba,
za ka dasa gonakin inabi ka kuma ci ’ya’yansu.
31 Sauran da suka rage na gidan Yahuda kuwa
za su yi saiwa a ƙarƙashi su kuma ba da ’ya’ya a bisa.
32 Gama daga Urushalima raguwa za tă fito,
kuma daga Dutsen Sihiyona ƙungiyar waɗanda suka tsira.
Himmar Ubangiji Maɗaukaki
zai cika wannan.
33 “Saboda haka ga abin da Ubangiji yana cewa game da sarkin Assuriya,
“Ba zai shiga wannan birni ba
ya harbe kibiya a nan.
Ba zai zo gabansa da garkuwa ba
ko ya gina mahaurai kewaye a kansa ba.
34 Ta hanyar da ya zo da ita zai koma;
ba zai shiga wannan birni ba,”
in ji Ubangiji.
35 “Zan kāre wannan birni in kuma cece shi,
saboda girmana da kuma saboda sunan Dawuda bawana!”
(2 Sarakuna 19.35-37)
36 Sai mala’ikan Ubangiji ya fita ya kuma karkashe mutane dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar a sansanin Assuriya. Sa’ad da mutane suka farka kashegari, sai ga gawawwaki duk a kwance! 37 Saboda haka Sennakerib sarkin Assuriya ya janye. Ya koma zuwa Ninebe ya zauna a can.
38 Wata rana, yayinda yake yin sujada a haikalin allahnsa Nisrok, ’ya’yansa maza Adrammelek da Sharezer suka kashe shi da takobi, suka kuma gudu zuwa ƙasar Ararat. Esar-Haddon ɗansa kuwa ya gāje shi a matsayin sarki.