10
Hadayar Kiristi sau ɗaya tak
1 Dokar, inuwa ce kawai ta kyawawan abubuwa masu zuwa, wannan inuwar ba ita ce ainihin abubuwan ba ne. Saboda haka ba za tă taɓa mai da masu matsowa kusa don yin sujada cikakku ta wurin irin hadayun da ake maimaitawa ba fasawa shekara-shekara ba. 2 Da a ce za tă iya, da ba su daina miƙa hadayu ba? Ai, da an riga an tsabtacce masu yin sujada sau ɗaya tak, da kuma ba za su ƙara damuwa da zunubansu ba. 3 Amma waɗancan hadayu abin tunawa da zunubai ne na kowace shekara, 4 domin ba zai taɓa yiwuwa jinin bijimai da na awaki yă kawar da zunubai ba.
5 Saboda haka, sa’ad da Kiristi ya shigo duniya ya ce,
“Hadaya da sadaka kam ba ka so,
sai dai ka tanadar mini jiki;
6 hadayun ƙonawa da kuma hadayun zunubi ba ka ji daɗin.
7 Sai na ce, ‘Ga ni nan, a rubuce yake cikin naɗaɗɗen littafi
na zo in aikata nufinka, ya Allah.’ ”* Zab 40.6-8 (dubi Seftuwajin)
8 Da farko ya ce, “Hadayu da sadakoki, hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka so, ba ka kuwa jin daɗinsu” (ko da yake doka ta bukaci a yi su). 9 Sa’an nan ya ce, “Ga ni nan, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon domin yă kafa na biyun. 10 Kuma bisa ga wannan nufi, aka mai da mu masu tsarki ta wurin miƙa hadayar jikin Yesu Kiristi sau ɗaya tak.
11 Kowace rana kowane firist yakan tsaya yin hidimar ibadarsa; sau da sau yakan miƙa hadayu iri ɗaya, waɗanda ba za su taɓa kawar da zunubai ba. 12 Amma da Kiristi ya miƙa hadaya ɗaya ta dukan lokaci saboda zunubai, sai ya zauna a hannun dama na Allah. 13 Tun daga lokacin nan yana jira a mai da abokan gābansa matashin ƙafafunsa, 14 gama ta wurin hadayan nan guda ɗaya ya kammala har abada waɗanda ake tsarkake.
15 Ruhu Mai Tsarki ma ya yi mana shaida game da wannan. Da farko ya ce,
16 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su
bayan wannan lokaci,
in ji Ubangiji.
Zan sa dokokina a cikin zukatansu,
in kuma rubuta su a kan zukatansu.Ӡ Irm 31.33
17 Sai ya ƙara da cewa,
“Zunubansu da kurakuransu
ba zan ƙara tunawa da su ba.”‡ Irm 31.34
18 In an gafarta zunubai, babu sauran bukatar miƙa hadaya.
Kira don a adana bangaskiya
19 Saboda haka, ’yan’uwa, da yake muna da wannan tabbaci na shiga Wuri Mafi Tsarki ta wurin jinin Yesu, 20 ta wurin sabuwa, rayayyiyar hanya kuma wadda aka buɗe mana ta labulen nan, wato, jikinsa, 21 da yake kuma muna da babban firist mai mulkin gidan Allah, 22 bari mu matso kusa da Allah da zuciya mai gaskiya da kuma cikakken tabbaci mai zuwa ta wurin bangaskiya. Bari mu bar zukatan da tsabta, lamirinmu babu mugunta, da kuma jikunanmu a wanke da ruwa. 23 Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne. 24 Bari kuma mu yi tunani a kan yadda za mu gargaɗe juna ga ƙauna da kuma ayyuka nagari. 25 Kada mu daina taruwa kamar yadda waɗansu suka saba, sai dai mu ƙarfafa juna, tun ba ma da kuka ga Ranan nan tana kusatowa ba.
26 Ba wata hadayar da za a yi don mutanen da suka yanke shawara su yi ci gaba da yin zunubi da gangan bayan sun sami sanin gaskiya. 27 A maimakon haka za su kasance da babban fargabar hukunci da kuma ta ƙunar wuta wadda za tă cinye abokan gāban Allah. 28 Duk wanda ya ƙi ya kiyaye dokar Musa akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidar mutum biyu ko uku. 29 Wane irin hukunci mai tsanani ne kuke tsammani zai dace da mutumin da ya nuna rashin bangirma ga Ɗan Allah, wanda ya yi banza da jinin nan na alkawarin da ya tsarkake shi, wanda kuma ya zargi Ruhun alheri? 30 Gama mun san shi, wannan wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce; zan rama,”§ M Sh 32.35 da kuma, “Ubangiji zai yi wa mutanensa hukunci.”* M Sh 32.36; Zab 135.14 31 Abu mai matuƙar bantsoro ne a fāɗa cikin hannuwan Allah mai rai.
32 Ku tuna da kwanakin nan da suka wuce bayan kun sami haske, sa’ad da kuka tsaya daram a tsananin shan wahala. 33 Wani lokaci a fili an tsananta muku aka kuma zage ku aka kuma tsananta muku; a wani lokaci kuma kuka tsaya tare da waɗanda aka yi musu haka. 34 Kuka ji tausayin waɗanda suke cikin kurkuku, da farin ciki kuma kuka yarda ku rabu da dukiyar da aka ƙwace muku, domin ku kanku kun san cewa kuna da madawwamiyar dukiya mafi kyau. 35 Saboda haka kada ku yar da tabbacinku; za a sāka muku a yalwace.
36 Kuna bukata ku jimre don sa’ad da kuka aikata nufin Allah, za ku karɓi abin da ya yi alkawari. 37 Gama,
“A cikin ɗan lokaci kaɗan,
mai zuwan nan zai zo
ba kuwa zai yi jinkiri ba.
38 Amma,
“Mai adalcina zai rayu ta wurin bangaskiya.
In kuwa ya ja da baya,
ba zan ji daɗinsa ba.”† Hab 2.3,4
39 Amma mu ba na waɗanda suke ja da baya, su kuma hallaka ba ne, amma na waɗanda suka gaskata, suka kuma sami ceto ne.