10
Annobar fāra
1 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu, 2 don kuma ku gaya wa ’ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji.”
3 Sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce masa, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Ibraniyawa ya ce, ‘Har yaushe za ka ƙi ƙasƙantar da kanka a gabana? Ka bar mutanena su tafi domin su yi mini sujada. 4 In ka ƙi ka bari su tafi, gobe zan aiko da fāra a ƙasarka. 5 Za su rufe fuskar ƙasar, har da ba za a iya ganin ƙasa ba. Za su cinye ɗan sauran abin da ya rage muku daga ɓarnar ƙanƙara, za su cinye dukan itatuwan da suke girma a gonakinku. 6 Za su cika gidajenka, da na fadawanka, da na dukan Masarawa, abin da iyayenka da kakanninka ba su taɓa gani ba, tun daga ranar da suka sami kansu a duniya, har yă zuwa yau.’ ” Sa’an nan Musa ya juya, ya rabu da Fir’auna.
7 Fadawan Fir’auna suka ce masa, “Har yaushe mutumin nan zai zama mana tarko? Ka bar mutanen su tafi domin su yi wa Ubangiji Allahnsu sujada. Har yanzu ba ka san cewa Masar ta lalace ba?”
8 Sa’an nan aka dawo da Musa da Haruna wurin Fir’auna. Sai ya ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji Allahnku sujada. Amma wa da wa za su tafi?”
9 Musa ya amsa, “Za mu tafi tare da ƙanananmu, da tsofaffinmu, da ’ya’yanmu maza da mata, da kuma garkunanmu na shanu da tumaki, gama dole ne mu yi bikin ga Ubangiji.”
10 Fir’auna ya ce, “Ubangiji ya taimaka bisa ga niyyarku, amma matanku da ƙanananku ba za su tafi ba! A fili yake kuna da niyyar mugunta. 11 Sam! Wannan ba zai taɓa yiwu ba, sai ko maza kaɗai su tafi su yi wa Ubangiji sujada, gama abin da kuke so ke nan.” Sa’an nan aka kori Musa da Haruna daga gaban Fir’auna.
12 Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka a bisa Masar domin fāra su sauko bisa ƙasar, su ci duk abin da yake girma a gonaki, duk abin da ƙanƙara ta rage.”
13 Saboda haka Musa ya miƙa sandansa bisa Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a kan ƙasar dukan dare da kuma dukan yini. Da safe kuwa iskar ta kawo fāra; 14 suka mamaye ƙasar duka, suka sauka a ko’ina a ƙasar. Ba a taɓa ganin annobar fāra haka ba, ba kuwa za a ƙara ganin fāra kamar haka ba. 15 Suka rufe ƙasar har ta zama baƙi. Suka cinye abin da ƙanƙara ta rage, kowane tsiron da yake girma a gonaki, da dukan ’ya’yan itatuwa. Babu ɗanyen abin da ya ragu a kan itatuwa ko tsire-tsire a dukan ƙasar Masar.
16 Fir’auna ya kira Musa da Haruna da gaggawa ya ce, “Na yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, na kuma yi muku. 17 Yanzu ku gafarta mini zunubina a wannan karo, ku kuma yi addu’a ga Ubangiji Allahnku yă ɗauke wannan muguwar annoba daga gare ni.”
18 Sai Musa ya bar Fir’auna ya kuma yi addu’a ga Ubangiji. 19 Sai Ubangiji ya canja iska zuwa iska mai ƙarfi ta yamma wadda ta ɗibi fārar zuwa Jan Teku. Babu fāran da suka rage a wani wuri a Masar. 20 Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, bai kuwa bar Isra’ilawa suka tafi ba.
Annobar duhu
21 Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Miƙa hannunka sama domin a yi duhu a bisa Masar, duhun da za a iya taɓawa.” 22 Sai Musa ya miƙa hannunsa sama, aka kuma yi duhu baƙi ƙirin bisa dukan ƙasar Masar na kwana uku. 23 Ba wanda ya iya gani wani ko yă bar wurinsa na kwana uku. Amma dukan Isra’ilawa sun kasance da haske a inda suke zama.
24 Sai Fir’auna ya aika aka kira Musa, ya kuma ce, “Ku tafi, ku yi wa Ubangiji sujada. Matanku da yaranku ma za su iya tafiya tare da ku; sai dai ku bar garkunanku na shanu da tumaki.”
25 Amma Musa ya ce, “Dole ka bari mu kasance da hadayu, da kuma hadayu na ƙonawa waɗanda za mu miƙa wa Ubangiji Allahnmu. 26 Dole dabbobinmu ma su tafi tare da mu; ko kofato ma, ba za a bari a baya ba. A cikinsu ne za mu ɗibi abin da za mu yi wa Ubangiji Allahnmu sujada. Ba mu kuma san irin abin da za mu miƙa wa Ubangiji ba, sai mun kai can.”
27 Amma Ubangiji ya taurare zuciyar Fir’auna, har bai yarda yă sake su ba. 28 Fir’auna ya ce wa Musa, “Fita, ka ba ni wuri! Ka mai da hankali, kada ka ƙara bayyana a gabana, gama ran da ka sāke ganin fuskata, a ran nan za ka mutu.”
29 Musa ya amsa, “Madalla, kamar yadda ka faɗa, ba zan ƙara bayyana a gabanka ba.”