12
Natan ya tsawata wa Dawuda
1 Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Da ya tafi wajensa, sai ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu a wani gari, ɗaya mai arziki, ɗayan kuma matalauci. 2 Mai arzikin yana da babban garken tumaki, da kuma shanu, 3 amma matalauci ba shi da kome sai ’yar tunkiyar da ya sayo. Ya yi kiwonta, ta kuwa yi girma tare shi da yaransa. Takan ci tare da shi ta sha ruwa a kwaf nasa, har ma ta kwanta a ƙirjinsa. Ta ma zama kamar ’ya a gare shi.
4 “To, sai ga wani baƙo ya zo wurin mai arzikin nan, amma mai arzikin ya ƙi yă kama tunkiyarsa, ko saniyarsa yă yanka don yă shirya wa baƙon da ya zo abinci. A maimako, sai ya je ya kama ’yar tunkiyan nan ta matalaucin ya yanka ya shirya wa mutumin da ya zo masa.”
5 Dawuda ya husata ƙwarai da mutumin, ya ce wa Natan, “Muddin Ubangiji yana a raye, mutumin da ya yi wannan ya cancanci yă mutu! 6 Dole yă biya diyyar tunkiyan nan sau huɗu, domin ya aikata haka ba tausayi.”
7 Sai Natan ya ce wa Dawuda, “Kai ne mutumin! Ga abin da Ubangiji, Allah ya ce, ‘Na naɗa ka sarki bisa Isra’ila, na kuma cece ka daga hannun Shawulu. 8 Na ba ka gidan maigidanka, da matan maigidanka duka. Na ba ka gidan Isra’ila da Yahuda. Da a ce dukan waɗannan sun kāsa maka, ai, da na ƙara maka. 9 Me ya sa ka rena maganar Ubangiji ta wurin yin mugunta haka a idonsa? Ka kashe Uriya mutumin Hitti da takobi, ka kuma ɗauki matarsa tă zama matarka. Ka kashe shi da takobin Ammonawa. 10 To, fa, takobi ba zai taɓa rabu da gidanka ba, domin ka rena ni, ka kuma ƙwace matar Uriya mutumin Hitti ta zama matarka.’
11 “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Daga cikin iyalinka zan kawo masifa a kanka. A idanunka zan ɗauki matanka in ba wa wani da yake kusa da kai, zai kuwa kwana da su da rana tsaka. 12 Ka aikata wannan a ɓoye, amma zan aikata wannan da rana tsaka, a gaban dukan Isra’ila.’ ”
13 Sai Dawuda ya ce wa Natan, “Na yi wa Ubangiji zunubi.”
Natan ya ce, “Ubangiji ya yafe maka zunubin. Ba za ka mutu ba. 14 Amma saboda ka yi haka ka sa abokan gāba suka rena Ubangiji,* Nassin Masoretik; wani daɗaɗɗen naɗaɗɗen littafin al’adar Ibraniyanci yana da wannan ka nuna cikakken reni wa Ubangiji. yaron da aka haifa maka zai mutu.”
15 Bayan Natan ya tafi gida, sai Ubangiji ya bugi yaron da matar Uriya ta haifa wa Dawuda, ya kuwa kamu da ciwo. 16 Dawuda ya roƙi Allah saboda yaron. Ya yi azumi, ya kuma shiga gidansa ya kwana kwance a ƙasa. 17 Dattawan iyalinsa suka tsaya kusa da shi don su ɗaga shi daga ƙasa, amma ya ƙi, bai kuwa ci wani abu tare da su ba.
18 A rana ta bakwai sai yaron ya rasu. Barorin Dawuda suka ji tsoro su gaya masa cewa yaron ya mutu, gama sun yi tunani cewa, “Yayinda yaron yake da rai, mun yi magana da Dawuda bai ji mu ba. Yaya za mu gaya masa yaron ya mutu? Ai, zai yi wa kansa ɓarna.”
19 Dawuda ya gane bayinsa suna wa juna raɗan wani abu, sai ya gane yaron ya mutu. Sai ya ce, “Yaron ya rasu ko?”
Suka ce, “I, ya rasu.”
20 Sa’an nan Dawuda ya tashi daga ƙasa. Bayan ya yi wanka, ya shafa mai, ya kuma canja rigunarsa, sa’an nan ya shiga gidan Ubangiji ya yi sujada. Sai ya tafi gidansa, ya nemi a ba shi abinci, aka ba shi, ya kuwa ci.
21 Barorinsa suka ce masa, “Me ya sa kake yin haka? Yayinda yaron yake da rai, ka yi azumi, ka kuma yi kuka, amma yanzu da yaron ya mutu, ka tashi, ka kuma ci abinci!”
22 Ya ce musu, “Yayinda yaron yake da rai, na yi azumi, na kuma yi kuka. Na yi tunani na ce, ‘Wa ya sani? Ko Ubangiji zai yi mini alheri yă bar yaron yă rayu.’ 23 Amma yanzu da ya mutu, me zai sa in yi azumi? Zan iya dawo da shi ne? Ni zan je wajensa, ba shi zai dawo wurina ba.”
24 Sai Dawuda ya yi wa matarsa Batsheba ta’aziyya, ya kuma tafi wurinta ya kwana da ita. Ta kuma haifi ɗa, suka ba shi suna Solomon. Ubangiji ya ƙaunace shi; 25 kuma saboda Ubangiji ya ƙaunace shi, sai ya aika da saƙo ta wurin annabi Natan yă ba shi suna Yedidiya.† Yedidiya yana nufin ƙaunace na Ubangiji.
(1 Tarihi 20.1-3)
26 Ana cikin haka, sai Yowab ya yi yaƙi da Rabba na Ammonawa, ya kuma ƙwace babban birnin. 27 Sa’an nan Yowab ya aika manzanni wurin Dawuda yana cewa, “Na yaƙi Rabba na kuma ƙwace hanyar samun ruwanta. 28 Yanzu fa ka tattara saura rundunoni ka fāɗa wa birnin ka ci shi. In ba haka ba zan karɓe birnin, a kuma kira shi da sunana.”
29 Saboda haka Dawuda ya tattara sauran rundunar sojojin suka tafi Rabba suka fāɗa masa suka kuma ci shi. 30 Ya ɗauke rawanin daga kan sarkinsu,‡ Ko kuwa na Milkom (wato, Molek). nauyinsa ya kai talenti§ Wato, wajen fam 75 (wajen kilo 34), na zinariya, an kuma yi masa ado da duwatsu masu daraja, aka aza shi a kan Dawuda. Ya kuma kwashe ganima mai yawa daga garin. 31 Ya fito da mutanen da suke a can, ya sa su su yi aiki da zarto, da diga, da kuma gatari, ya kuma sa su bugan bulok. Haka ya yi wa dukan garuruwan Ammonawa. Sa’an nan Dawuda da dukan sojoji suka koma Urushalima.