20
Ciwon Hezekiya
(2 Tarihi 32.24-26; Ishaya 38.1-8,21,22)
1 A kwanakin nan sai Hezekiya ya kamu da rashin lafiya har ya kusa mutuwa. Sai annabi Ishaya ɗan Amoz ya zo wurinsa ya ce, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ka kintsa gidanka domin za ka mutu, ba za ka warke ba.”
2 Hezekiya ya juya fuskarsa wajen bango ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, 3 “Ya Ubangiji, ka tuna yadda na yi tafiya a gabanka da aminci da zuciya ɗaya, na kuma aikata abin da yake daidai a gabanka.” Sai Hezekiya ya yi kuka mai zafi.
4 Kafin Ishaya yă bar tsakiyar filin gida, sai maganar Ubangiji ta zo masa cewa, 5 “Ka koma ka ce wa Hezekiya, shugaban mutanena, ‘Ga abin da Ubangiji Allah na mahaifinka Dawuda ya ce, na ji addu’arka na kuma ga hawayenka; zan warkar da kai. A rana ta uku daga yau za ka haura zuwa haikalin Ubangiji. 6 Zan ƙara maka shekara goma sha biyar. Zan kuma cece ka daga hannun sarkin Assuriya. Zan kāre birnin nan saboda kaina da kuma bawana Dawuda.’ ”
7 Sai Ishaya ya ce, “A kwaɓa ɓaure.” Sai aka yi haka, aka shafa wa marurun, ya kuma warke.
8 Hezekiya ya tambayi Ishaya, “Wace alama ce za tă nuna cewa Ubangiji zai warkar da ni, kuma cewa in tafi haikalin Ubangiji kwana uku daga yanzu?”
9 Sai Ishaya ya ce, “Ga alamar Ubangiji zuwa gare ka da za tă nuna cewa Ubangiji zai cika alkawarinsa. Kana so inuwa tă yi gaba da taki goma, ko tă koma baya da taki goma?”
10 “Ai, abu mai sauƙi ne inuwa tă yi gaba da taki goma.” In ji Hezekiya, “Gwamma dai tă koma baya da taki goma.”
11 Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa inuwa ta koma baya da taki goma bisa ga magwajin rana wanda Sarki Ahaz ya gina.
Jakadu daga Babilon
(Ishaya 39.1-8)
12 A wannan lokaci, Merodak-Baladan ɗan Baladan sarkin Babilon ya aika wa Hezekiya wasiƙu tare da kyauta, domin ya sami labarin rashin lafiyar Hezekiya. 13 Hezekiya ya karɓi jakadun, ya nuna musu dukan abin da yake a ɗakunan ajiyarsa, azurfa, zinariya, kayan ƙanshi da mai, wurin ajiye makamansa da kuma dukan abin da aka samu a ɗakin ajiyarsa. Babu wani abu a fadansa ko a dukan mulkinsa da Hezekiya bai nuna musu ba.
14 Sai annabi Ishaya ya tafi wurin Sarki Hezekiya ya tambaye shi ya ce, “Me mutanen nan suka ce, kuma daga ina suka fito?”
Sai Hezekiya ya ce, “Daga ƙasa mai nisa. Daga Babilon.”
15 Annabin ya yi tambaya, “Me suka gani a fadanka?”
Hezekiya ya ce, “Ba abin da yake a ma’ajina da ban nuna musu ba.”
16 Sai Ishaya ya ce wa Hezekiya, “Ka ji kalmar Ubangiji. 17 Lokaci yana zuwa da za a kwashe kome a fadanka da kuma dukan abubuwan da kakanninka suka tara har yă zuwa yau, a kai su Babilon. Ba abin da za a rage, in ji Ubangiji. 18 Za a kuma kwashe waɗansu daga cikin zuriyarka, na jiki da jininka waɗanda za a haifa maka, su zama bābānni a fadan sarkin Babilon.”
19 Hezekiya ya ce, “Maganar Ubangiji da ka faɗa ta yi kyau.” Gama ya yi tunani cewa, “Ai, ba ni da damuwa, tun da yake za a yi zaman lafiya da salama a kwanakina.”
(2 Tarihi 32.32,33)
20 Game da sauran ayyukan mulkin Hezekiya, dukan nasarorinsa da yadda ya yi tafki da kuma bututun ruwa inda ya kawo ruwa cikin birni, duk a rubuce suke a cikin littafin tarihin sarakunan Yahuda. 21 Hezekiya ya huta tare da kakanninsa. Manasse ɗansa kuma ya gāje shi.