5
Bangaskiya cikin Ɗan Allah
1 Kowa ya gaskata cewa Yesu shi ne Kiristi, shi haifaffe na Allah ne, kuma duk mai ƙaunar mahaifi kuwa, yakan ƙaunaci ɗansa ma. 2 Ga yadda muka san cewa muna ƙaunar ’ya’yan Allah. Muna yin haka ta wurin ƙaunar Allah da kuma aikata umarnansa. 3 Ƙaunar Allah ita ce, a yi biyayya da umarnansa. Umarnansa kuwa ba masu nauyi ba ne; 4 domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya. 5 Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.
6 Ga wanda ya zo ta wurin ruwa da jini, wato, Yesu Kiristi. Bai zo ta wurin ruwa kaɗai ba, sai dai ta wurin ruwa da kuma jini. Ruhu ne kuwa yake ba da shaida, gama Ruhu shi ne gaskiya. 7 Akwai shaidu uku, wato, 8 Ruhu,* Rubuce-rubucen hannu na baya-bayan nan na Bulget shaida a sama: Uba, Kalma da kuma Ruhu Mai Tsarki, waɗannan uku kuwa ɗaya ne. 8 Akwai kuma uku da suka ba da shaida a duniya, wannan: Ruhu (babu kalman nan a rubuce-rubucen hannu na Girik kafin karni na goma sha shida) da ruwa, da kuma jini; waɗannan uku kuwa manufarsu ɗaya ce. 9 Tun da yake mukan yarda da shaida mutane, ai, shaidar Allah ta fi ƙarfi. Wannan ita ce shaidar Allah, wato, ya shaidi Ɗansa. 10 Duk wanda ya gaskata da Ɗan Allah, yana da shaidan nan a zuciyarsa. Duk wanda bai gaskata da Allah ba kuwa ya mai da shi maƙaryaci, domin bai gaskata shaidar da Allah ya bayar game da Ɗansa ba. 11 Wannan kuwa ita ce shaidar; cewa Allah ya ba mu rai madawwami, wannan rai kuwa yana cikin Ɗansa. 12 Duk wanda yake da Ɗan, yana da rai; wanda kuwa ba shi da Ɗan Allah, ba shi da rai.
Ƙarshen magana
13 Ina rubuta waɗannan abubuwa gare ku, ku da kuka gaskata sunan Ɗan Allah domin ku san kuna da rai madawwami. 14 Wannan shi ne ƙarfin halin da muke da shi sa’ad da muke zuwa a gaban Allah, gama mun san cewa kome muka roƙa bisa ga nufinsa, yakan saurare mu. 15 In kuwa muka san cewa yana sauraranmu, ko mene ne muka roƙa, mun sani, mun riga mun sami abin da muka roƙa daga gare shi ke nan.
16 Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba. 17 Duk rashin adalci, zunubi ne, amma akwai waɗansu zunuban da ba sa kai ga mutuwa.
18 Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba. 19 Mun san cewa mu ’ya’yan Allah ne, duniya duka kuwa tana hannun Mugun. 20 Mun san cewa Ɗan Allah ya zo duniya, ya kuma ba mu ganewa domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna cikinsa, shi da yake Allah na gaskiya wato, cikin Ɗansa Yesu Kiristi. Shi ne Allah na gaskiya da kuma rai na har abada.
21 ’Ya’yana ƙaunatattu, ku yi nesa da gumaka.
*5:8 Rubuce-rubucen hannu na baya-bayan nan na Bulget shaida a sama: Uba, Kalma da kuma Ruhu Mai Tsarki, waɗannan uku kuwa ɗaya ne. 8 Akwai kuma uku da suka ba da shaida a duniya, wannan: Ruhu (babu kalman nan a rubuce-rubucen hannu na Girik kafin karni na goma sha shida)