9
1 Haka aka lissafta dukan Isra’ila a tarihin zuriyoyi a littafin sarakunan Isra’ila. Aka kwasa mutanen Yahuda zuwa zaman bauta a Babilon domin rashin aminci.
Mutanen Urushalima
2 To, na farkon da aka sāke zaunar da su a mallakarsu a garuruwansu, su ne waɗansu Isra’ilawa, firistoci, Lawiyawa da kuma masu hidimar haikali.
3 Waɗanda suke daga Yahuda, daga Benyamin, da kuma daga Efraim da Manasse waɗanda suka zauna a Urushalima su ne,
4 Uttai ɗan Ammihud, ɗan Omri, ɗan Imri, ɗan Bani, zuriyar Ferez ɗan Yahuda.
5 Na mutanen Shilo kuwa su ne,
Asahiya ɗan fari da ’ya’yansa maza.
6 Na mutanen Zera su ne,
Yewuyel.
Mutane daga Yahuda sun kai 690.
7 Na Benyamin su ne,
Sallu ɗan Meshullam, ɗan Hodawiya, ɗan Hassenuwa;
8 Ibnehiya ɗan Yeroham;
Ela ɗan Uzzi, ɗan Mikri;
da Meshullam ɗan Shefatiya, ɗan Reyuwel, ɗan Ibniya.
9 Mutane daga Benyamin, kamar yadda aka lissafta zuriyarsu, sun kai 956. Dukan waɗannan mutane kawunan iyalansu ne.
10 Na firistoci su ne,
Yedahiya; Yehoyarib; Yakin;
11 Azariya ɗan Hilkiya, ɗan Meshullam, ɗan Zadok, ɗan Merahiyot, ɗan Ahitub, shugaban da yake lura da gidan Allah;
12 Adahiya ɗan Yeroham, ɗan Fashhur, ɗan Malkiya;
da Ma’asai ɗan Adiyel, ɗan Yazera, ɗan Meshullam, ɗan Meshillemit, ɗan Immer.
13 Firistocin da suke kawunan iyalai, sun kai 1,760. Dukansu ƙwararru ne, masu hakkin hidima a cikin gidan Allah.
14 Na Lawiyawa su ne,
Shemahiya ɗan Hasshub, ɗan Azrikam, ɗan Hashabiya, mutumin Merari;
15 Bakbakkar, Heresh, Galal da Mattaniya ɗan Mika, ɗan Zikri, ɗan Asaf;
16 Obadiya ɗan Shemahiya, ɗan Galal, ɗan Yedutun;
da Berekiya ɗan Asa, ɗan Elkana, wanda ya zauna a ƙauyukan Netofawa.
17 Matsaran ƙofofi su ne,
Shallum, Akkub, Talmon, Ahiman da ’yan’uwansu. Shallum ne babbansu 18 da aka ajiye a Ƙofar Sarki a gabas, har zuwa wannan lokaci. Waɗannan su ne matsaran ƙofofi na sansanin Lawiyawa.
19 Shallum ɗan Kore, ɗan Ebiyasaf, ɗan Kora, da ’yan’uwansa matsaran ƙofofi daga iyalin (mutanen Kohat) su suke da hakkin tsaron madogaran ƙofar Tenti kamar dai yadda kakanninsu suka kasance da hakkin tsaron mashigin mazaunin Ubangiji.
20 A dā Finehas ɗan Eleyazar ne yake lura da matsaran, kuma Ubangiji ya kasance tare da shi.
21 Zakariya ɗan Meshelemiya shi ne mai tsaro a mashigin Tentin Sujada.
22 Duka-duka, waɗanda aka zaɓa don su zama matsaran madogaran ƙofa sun kai 212. Aka rubuta su zuriya-zuriya a ƙauyukansu.
Dawuda da Sama’ila mai duba ne suka sa matsaran a wurarensu na aminci. 23 Su da zuriyarsu, su suke lura da tsaron ƙofofin gidan Ubangiji, gidan da ake kira Tenti. 24 Matsaran suna a kusurwoyi huɗu, gabas, yamma, arewa da kudu. 25 ’Yan’uwansu a ƙauyukansu sukan zo lokaci, lokaci su yi ayyukansu kwana bakwai, bakwai. 26 Amma manyan matsara huɗu, waɗanda suke Lawiyawa, an danƙa musu hakkin lura da ɗakuna da kuma wuraren ajiya a gidan Allah. 27 Sukan kwana a kewayen gidan Allah, domin dole su tsare shi; kuma su suke lura da mabuɗi don buɗewa a kowace safiya.
28 Waɗansunsu su ne suke lura da kayayyakin da ake amfani da su a hidimar haikali; sukan ƙirga su sa’ad da ake shigar da su da sa’ad da ake fitar da su. 29 An sa waɗansu su lura da kayayyakin da kuma dukan waɗansu kayan wuri mai tsarki, da kuma gari da ruwan inabi, da mai, turare da kuma kayan yaji. 30 Amma waɗansu firistoci ne suke harhaɗa kayan yajin. 31 Wani Balawe mai suna Mattitiya, ɗan farin Shallum mutumin Kora ne aka danƙa masa hakkin toya burodin miƙawa. 32 Waɗansu ’yan’uwansu Kohatawa ne suke lura da shiryawa burodin da ake kaiwa a tebur a kowane Asabbaci.
33 Waɗanda suke mawaƙa, kawunan iyalan Lawiyawa, sukan zauna a ɗakunan haikali kuma ba sa yin waɗansu ayyuka domin su suke da hakkin aiki dare da rana.
34 Dukan waɗannan su ne kawunan iyalan Lawiyawa, manya kamar yadda aka lissafta su a zuriyarsu, kuma suna zama a Urushalima.
Zuriyar Shawulu
(1 Tarihi 8.29-38)
35 Yehiyel mahaifin Gibeyon ya zauna a Gibeyon.
Matarsa ita ce Ma’aka 36 ɗansa na fari kuwa shi ne Abdon, sai Zur, Kish, Ba’al, Ner, Nadab, 37 Gedor, Ahiyo, Zakariya da Miklot. 38 Miklot shi ne mahaifin Shimeyam. Su ma sun zauna kusa da danginsu a Urushalima.
39 Ner shi mahaifin Kish, Kish mahaifin Shawulu, kuma Shawulu shi ne mahaifin Yonatan, Malki-Shuwa, Abinadab da Esh-Ba’al.* Aka kuma sani da Ish-Boshet
40 Ɗan Yonatan shi ne,
Merib-Ba’al wanda shi ne mahaifin Mika.
41 ’Ya’yan Mika maza su ne,
Fiton, Melek, Tareya da Ahaz.
42 Ahaz shi ne mahaifin Yada, Yada shi ne mahaifin Alemet, Azmawet da Zimri, Zimri kuwa shi ne mahaifin Moza. 43 Moza shi ne mahaifin Bineya; Refahiya, Eleyasa da kuma Azel.
44 Azel yana da ’ya’ya maza shida, kuma ga sunayensu.
Azrikam, Bokeru, Ishmayel, Sheyariya, Obadiya da Hanan. Waɗannan su ne ’ya’yan Azel maza.